EFCC ta gano ma'aikatan bogi 37,395
Hukumar da ke yaki
da masu yi wa tattalin arzikin Nigeria zagon-kasa, EFCC ta ce ta gano
ma'aikatan gwamnatin tarayya na bogi su dubu 37, 395.
Shugaban
hukumar Ibrahim Magu ya ce sun gano wadannan mutanen ne a wani aikin
hadin gwiwa da ma'aikatar kudi da kuma ofishin babban Akawun gwamnatin
tarayya, yana mai cewa hakan ya sa gwamnatin tarayya ta yi asarar kusan
Naira biliyan daya.
A cewar hukumar, za a ci gaba da gano ma'aikatan bogi a yayin da suke ci gaba da bincike a rijistar albashin ma'aikatun gwamnatin tarayya.
A baya dai, ministar kudi, Kemi Adeosun, ta ce an gano dubban ma'aikatan bogi a kasar.

Comments
Post a Comment