An Tsare Jami'an Tsaro akan zargin Fyaɗe

Daga Munkaila T. Abdullah, Dutse
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Jigawa ta bada tabbacin tsare wani Jami’insu tareda wani jami’in hukumar tsaro na farin kaya (NSCDC) bisa zargin yiwa wata mata fyaɗe akan iyakar Nijeriya da Nijar dake ƙaramar hukumar Maigatarin jihar Jigawa.
Kakakin rundunar ta ‘Yan sanda reshen jihar ta Jigawa, SP Abdul Jinjiri ya tabbatar da tsare waɗannan jami’an tsaro su biyu a ya yin zantawarsa da manema ‎labarai a birnin Dutse..
Ya ce “‎Ya ce, babu ko shakka mun sami rahoton wannan badaƙala kuma tuni waɗanda ake zargi suna ɓangaren gudanarda bincike na wannan runduna tamu domin bibiya don binciko gaskiyar al’amari”.
Haka kuma ya ƙara da cewa,‎ wannan baiwar Allah ta gabatar da ƙorafinta ga cibiyar jami’anmu dake garin Maigatari wadda a yanzu haka an tsare waɗanda ake zargi domin gudanarda bincike.
Sannan ya ce, tunidai rundunar ta tura jami’anta har wannan waje domin cigaba da bincike kuma matuƙar aka tabbatar da faruwar wannan al’amari to babu ko shakka za’a hukuntasu kamar yadda dokar wannan runduna tamu dama kudun tsarin wannan‎ ƙasa ya tanada.
Kakakin ya bayyana sunayen waɗanda ake zargi wadda suka haɗarda Sajan Jamilu Muhammad da kuma Habu Musa wadda shi kuma Jami’in hukumar NSCDC ne, gamida ita kuma matar da aka yiwa fyaɗen mai suna Malama Safiya.
‎Ita kuwa Malama Safiya wadda aka yiwa wannan aika-aika ta bayyanawa manema labarai cewa, al’amarin ya afku ne a lokacin da ta dawo daga ƙasar Nijar kan hanyarta ta dawowa gida garin Maigatari.
Ta ce‎ “bayan da na kira mai babur ya ɗauko ni zuwa gida, muna cikin tafiya sai na ji jiri na ɗiba ta yadda na umarci mai babur da ya tsayi domin na ɗan huta, munan sai ga waɗannan jami’an tsaro su biyu yadda suka ce suna zarginmu da ni da wannan mata don haka sai mun basu cinhancin naira dubu goma”.
Ta cigaba da cewa “ nace musu bani da waɗannan kuɗaɗe sai naira ɗari biyar, kuma ni ba matar Aure bace mijina ya sakeni har ma na nuna musu takardar sakin amma suka ƙwace, suka sallami wannan mai babur ni kuma suka barni anan saida suka yi amfani da ni. Ni kuma shi ne na kai ƙara a bi min haƙƙina” inji ta.
“Sun tirsasani kan cewa, sai na basu waɗancan kuɗaɗe har naira dubu goma kafin su ƙyale ni in tafi ko kuma su yi amfani da ni yadda a nan ne suka tirsasni zuwa wani kango yadda suka yi amfani da ni” inji Safiya.
Rahotanni dai sun bayyana cewa,‎ sajan Jamilu da takwaransa Habu waɗanda ake zargi sun baro wajen aikinsu na ainihi yadda suka fito fatirol har suka yi arba da wannan mata kuma suka farmata..
daga: http://hausa.leadership.ng/2017/10/25/tsare-%C9%97an-sanda-da-jamiin-nscdc-bisa-zargin-yi-wa-bazawara-fya%C9%97e/

Comments

Popular posts from this blog

Body Language :: Hand to face gestures

Treaty In Dubai To Legalize Same Sex Marriage — Nigeria Christians Cry Out

Nigeria's VP Yemi Osinbajo stays home due to conflicting schedules with president