Catalonia ta fice daga Kasar Spaniya

Yar Catalonia Hakkin mallakar hoto Getty Images

Image caption 
Magoya bayan ballewar yankin
sun taru a gaban majalisar a lokacin da ake kada kuri'ar

Majalisar dokokin yankin Catalonia na Spaniya ta kada kuri'ar ballewa daga kasar baki daya domin kafa kasarsu.
Matakin ya samu goyon bayan 'yan majalisa 70 daga cikin 80 yayin da 'yan adawa suka kauracewa zaman.
Tun da farko Fira Ministan Spaniya Mariano Rajoy ya shaida wa 'yan majalisar dattawa cewa ana bukatar kawar da kwarya-kwaryar 'yancin da yankin yake da shi domin dawo da "doka, da demokuradiyya da kuma zaman lafiya" a Catalonia.
Wannan rikici ya barke ne lokacin da jama'ar yankin suka kada kuri'a mai cike da rudani a farkon watan nan, inda suka amince da kafa kasarsu mai cin gashin kanta.
Gwamnatin Catalonia ta ce daga cikin kashi 43 cikin dari na wadanda suka kada kuri'a a zaben raba gardamar, kashi 90 ne suka goyi bayan a balle.
Sai dai kotun tsarin mulki ta Spain ta yanke hukuncin cewa kuri'ar ta sabawa doka.
Gwamnatin Catalonia ta ce daga cikin kashi 43 cikin dari na wadanda suka kada kuri'a a zaben raba gardamar, kashi 90 ne suka goyi bayan a balle.
Sai dai kotun tsarin mulki ta Spainiya ta yanke hukuncin cewa kuri'ar ta saba wa doka.

Me gwamnatin Spaniya za ta yi nan gaba?

Jim kadan bayan kada kuri'ar amincewa da kafa kasar ta Catalonia, majalisar dattawan Spaniya ta amince da matakin da ya bai wa gwamnatin kasar damar kwace iko da mulkin Catalonia.
'Yan majalisa 214 ne suka amince da matakin yayin da 47 suka yi watsi da shi.
Da yake daukar alkawarin dawo da doka da oda a Catalonia, Mista Rajoy, ya ce "sama da shekara 40 Spaniya ta kasance babbar mai fada aji ta fuskar tattalin arziki, a don haka Catalonia ba za ta karya wannan tarihi ba".
Ya kira taron majalisar zartaswa domin duba matakan da zai dauka.
Za su iya hada wa da korar shugabannin Catalonia, abin da zai bai wa gwamnatin Spaniya kwace iko da harkokin kudaden yankin, da rundunar 'yan sanda da kuma kafafen yada labarai na gwamnati.

Source: http://www.bbc.com/hausa/labarai-41780738

Comments

Popular posts from this blog

'Women Tax Free' - The shop where men pay 7% more

Body Language :: Hand to face gestures

ABU/SBRS 2017-2018 SESSION REGISTRATION PROCEDURE