Shaidanun Mata 10 A Duniya. Ganinku Ba Alheri Ba



Shaidanun Mata 10 Da Suka Yi Kaurin Suna A Duniya
Daga Wakilinmu
Mafi yawancin mutane sun yi imanin cewar mata an san su ne da tausayi da nuna kauna ga al’umma. Ga su kuma da nuna son jan aji. Sai dai, an samu akasi na nuna irin wadanan kyawawan halayen ga wasu mata goma da alkalumma suka nuna sun zarce saura a shedana, wadanda ba abin da suka fi jin dadi a
duniya tamkar zubar da jinin mutane.Wannan dabi’ar tasu, ta zama barazana ga duniya. Matan, sun hallaka manya da yara ta muggan hanyoyi da nau’uka mabambanta.
A lokuta da yawa, mu kan shafawa idonmu toka ta hanyar kallon ta’addancin da ake gani wasu shedanu   maza ke aikatawa a doron kasa, tare kuma da alakanta duk wata barna, shedana da kauce hanya ga mazan a mafiya yawan lokuta.
Wannan sharhi ne akan mata shedanu goma da suka kafa tarihi wurin hallaka jama’a a duniya, rahoton zai warware zare da abawa akan wadannan gogaggun shaidanun mata goma. Matan su ne:

  1. Irma Ida Ilse Grese
An haife ta ranar bakwai ga watan Oktoba na shekarar 1923, a jihar Wrechen Free dake kasar Jamus, ta mutu ranar 13 ga watan Disambar shekarar 1945, a garin Hamelin, dake kasar ta Jamus.
Marigayar an dauke ta aikin gandiroba ne a sashen mata dake Bergen-Belsen dake sansanin ‘yan gudun hijira na Yahudawa. An yanke mata hukuncin kisa saboda azabtar da ‘yan bursuna. An kashe ta tana da shekaru 22, kuma itace mace mai karancin shekaru da aka kashe a bisa hukuncin kundin shari’ar mulkin Jamus a karni na ashirin a ranar 13 ga watan Disambar shekarar 1945, a garin Hamelin. Irma ana yi mata lakabi da ‘Kyakkywar Takadarar Belsen’, ana kuma yi mata kirari da ‘Kurar Auschwitz, ba ki ci da gashi’. Irma, tantiyar Karuwa ce, sannan kuma jigo a harkar safarar kwayoyi.
Ta kashe mutane marasa adadi, wasu ma daga cikinsu kwastomominta na alfasha ne. bayan ta shiga komar hukuma, ta shaidawa kotu cewa zuciyarta kan raya mata kisan kai, kuma duk lokacin da wannan sha’awa ta motsa, toh babu makawa sai ta kashe mutum.

  1. Myra Hindley
An haifi Myra a shekarar 1942, a kasar Ingila. Myra, ta nemi taimakon kawarta Ian Brady, suka aikata fyade da kashe yara uku dukkaninsu ‘yan shekaru 12 a duniya, tare da kuma hallaka matasa biyu masu shekaru 16 da 17, ta kuma yi kaurin suna wurin yin garkuwa da mutane.
Wani surikinta mai shekaru 17 ya taba yi mata cinnen ‘yan sanda, akan kisan kai har sau uku inda karara Hindley ta amsa laifin aka kuma yanke mata hukuncin daurin rai da rai. A shekarar 2002 aka kai ta gidan ta kaso domin ta karasa rayuwarta a can. Har bayan yanke mata wannan hukuncin, Myra ba ta nuna saduda ko nadama ba a ayyukanta. Don haka ne ma ake yi mata lakabi da tauraruwa mai wutsiya.

  1. Isabella Castile
Isabella mai bin darikar Cocin Katolika ce, an haife ta a shekarar 1451, ta mutu a shekarar 1504 kuma sarauniya ce a Castile León. Mijinta mai suna Ferdinand yana rike da sarautar Basarake ne na biyu na garin Aragon, a lokacinsa ya jajirce wajen tabbar da kawo zaman lafiya a daulolin da suka haifar da samuwar hada kan kasar Sifaniya.
Tayi amfani da mukamin mijin nata tayi sanadiyyar azalzalawa musulmi da Yahudawa suka yi gudun hijira, ta kuma dauki nauyin Christopher Columbus a shekarar 1492, wanda hakan ya janyo kafa sabuwar duniya. Ta shekar da jinanen al’umma wuce misali. Mace ce da ke jin samun annushuwa game da shan jini da cin naman mutane.

  1. Beberly Gail Allitt
Tana daya daga cikin jerin shaidanun mata a duniya, wurin hallaka mutane kuma ana yi mata lakabi da Mala’ikar mutuwa. Haifaffiyar kasar Ingila, Beberly an yake mata hukunci saboda kashe yara hudu da yunkurin hallaka wasu yara uku, tare da ji wa wasu yara shida munanan raunuka. Duk wadannan laifukan ta tabka su ne a cikin kwanaki 59 daga watan Fabrairu zuwa watan Afrilun shekarar 1991. Mai shari’a Mista Latham na kotun dake Nottingham, ya yanke mata hukuncin kisa sakamakon kashe yara marasa lafiya da aka kwantar a asibitin da take aiki a matsayin Nas mai suna Grantham dake Kesteben Lincolnshire.
Ta hallaka yaran ne ta hanyar basu maganin insulin da ya wuce ka’ida, inda yaran suka kamu da wata irin cuta da jami’an ‘yan sanda, suka kasa gano yadda ta aikata ta’asar. An yanke mata hukunci cikin watan Mayun shekarar 1993 inda alkalin ya ce, zamanta a cikin al’umma, babban hadari ne. An yi mata daurin talala a asibitin ‘Rampton Secure’ da ke Nottinghamshire.

  1. Sarauniya Mary I
Ita ma tana daya daga cikin gaggan shaidanu mata a duniya, tana rike da sarautar gargajiya ta Mary ta daya kuma an haife ta ne ranar 18 ga watan Fabrairun shekarar 1516, inda kuma ta mutu ranar 17 ga watan  Nuwambar shekarar 1558. Ta zama sarauniyar kasar Ingila da kasar Ireland watan juli na shekarar 1553 har ya zuwa lokacin mutuwarta.
Sakamakon yiwa mabiya Cocin ‘yan tawaye kisan gilla, Sarauniya Mary ‘yan hammayarta, suna yi mata lakabi da Mary mai zubar da jini. Ita ce kadai ‘yar da auren ta da Sarki Henry na takwas, ya samu matsala da kuma matarsa ta farko Catherine ‘yar garin Aragon. Za a iya tuna Mary ne, saboda rawar da ta taka ta hanyar dabar da ta yi na mayar da kasar Ingila kan turbar darikar Katolika. A lokacinta, an hallaka jiga-jigan mabiya Cocin ‘yan tawaye. Don gujewa kisan gilla, sama da mabiya Coccin ‘yan tawaye su 800 ne suka yi gudun hijira daga Ingila, inda sai da bayan ta mutu ne suka dawo kasar ta Ingila.

  1. Belle Gunness
Itama tana daga cikin sahun shaidanun matan 10 da suka yi kaurin suna a duniya wurin daukar rayukan jama’a. Belle mai tsawon kafa shida da nauyin kilo 90 kakkarfa ce. Tana da karfin mulki kuma jika ce a Norwegian. An yi has ashen ita ce ta hallaka mijinta da dukkan ‘ya’yansu a lokuta mabambanta, an kuma tabbatar ita ce ta kashe zawarorinta da samarinta da kuma ‘ya’yanta mata Myrtle da Lucy.
Belle ta tabka ta’addancin ne don nuna zalamarta a fili na mallake dukkanin dukiya da kadarorin zawarawan nata a bisa shirin inshore na sace kudi da kaddara don su zama mallakarta. Rahotanni sun bayyana cewa Belle, ta kashe mutane kusan 20 a karni da dama da suka shige, wasu kuma sun yi ikirarin ta hallaka sama da mutane 100.
Binciken da masana suka gudanar akan gawarwakin mutanen da Belle ta kashe, ya tona rashin wayonta a fili saboda gawar mutum biyu daga cikin wadanda ta kashe, inci biyu ce da tsawon Belle inda hakan ya sanya sunanta ya shiga kudin gaggan masu aikata laifin kisa na Amurka.

  1. Mary Ann Cotton
An haife ta a watan Oktoba na shekarar 1832 a wata anguwa mai suna Moorsley dake Durham kuma ita ce ‘yar kasar Birtaniya ta farko, da ta rinka hallaka jama’a kuma ta auri William Mowbray, tana da shekara 20. Mace ce mai Kaudi, ta tare da angon nata William a garin Debon, inda ta haifa masa ‘ya’ya biyar; hudu daga ciki suka mutu sakamakon wani zazzabi mai zafi da kuma ciwon ciki. Komawarsu Arewa maso gabas din kasar nan ma ba ta sake zani ba. Inda ta kara haifawa William ‘ya’yansu uku, kuma uku suka mutu. Ana nan kuma, William shima a watan Janairun shekarar 1865 ya sheka lahira sakamakon wata cuta mai kama da ciwon kwakwalwa. Ganin cigaba da aukuwar lamarin, wani sashen bin diddigin kula da kashe kudin gwamnati na kasar, ya yi gaggawar amince da a kashe Fam talatin da biyar don gano musabbabin yawan mace-macen. An gano mijin Ann na biyu mai suna George Ward shima ya mutu ne ta hanyar cuta mai kama da ciwon kwakwalwa.
Bugu da kari, ta haka ne su ma sauran ‘ya’yanta biyu suka mutu. Bayan zurfafa binciken da wasu jaridun kasar suka dukufa akai ne, suka bankado lokacin da Ann ta koma arewacin kasar ingila da zama, mazan da ta aura su uku suma sun mutu da wani saurayin daya da mahaifiyarta da kuma dukkan yaran da ta haifa arewacin kasar ta Ingila duk sun mutu ne ta hanyar ciwon ciki. Ranar 24 na watan Maris din shekarar 1873 aka rataye Ann a Durham a bisa hallaka rayukan jama’a ta hanyar zuba musu guba.
Wanda ya rataye ta a gidan yarin kasar, yayi ta jan igiyar ratayar a hankali don dandanawa Ann radadin yadda zafin fitar rai yake.

  1. Ilse Koch
Ana yi mata lakabi da mutuwa kuma ko kuma Mayar Buchenwald. Ranar 22 ga watan Satumbar shekarar 1906, ta auri Karl-Otto Koch. Ilse sananniyar ‘yar jinsin Yahudawa ce, kuma ta farko da rundunar sojin Amurka suka taba yanke wa hukunci. Ta dinga fakewa da matsayin da mijinta Koch ke rike dashi a kasar inda ta dinga hallaka jama’a. Ta kware wurin sace kayayyakin ‘yan bursunan da ta kashe inda ta gina katafaren dakin wasa a shekarar 1940, da Fam 250,000 da aka yiwa alamar shaida da ta sace a jikin ‘yan bursunan data kashe. An bada mukamin babbar mai sa ido ta mata bursuna dake Buchenwald. Ta hallaka kanta ne ta hanyar rataye kanta a gidan yari na mata dake Aichach ranar daya ga watan Satumbar 1967.

  1. Katherine Knight
Tana daya daga cikin fitattun shaidanun mata 10, an haife ta ranar 24 ga watan Oktoban shekarar 1955 ta kuma kare sauran rayuwarta a gidan Kaso. An yanke mata daurin rai da rai ba tare da gudanar da wata shari’a ba. Ta kashe daya daga cikin mazan da ta aura ta hanyar yi masa yankan Rago ta kuma daddabawa wani mijin nata Thomas wuka har sau 37 sannan ta fede shi ta shanya kuma ta kyafe namanshi ta yanke masa kai da duwawunshi tai farfesunsu da nufin ba ‘ya’yanta su ci, inda ‘yan sanda suka gano ta’addancin nata daga baya.

  1. Elizabeth Bathory
Tana daya daga cikin jerin shaidanun mata goma a duniya a tarihin kasar Hangariya da ta kafa tarihi wurin yiwa mutane kisan gilla. An haifi Eli ne a shekarar 1560 ta kuma mutu a shekarar 1614. Ta fito ne daga sanannen gidan sarautar Countess ta Daular kasar Hangariya. Tana kashe ‘yan mata ne ta hanyar mummunan duka da kona su da canza fasalin fuskokin matan da kuma azabtar dasu ta hanyoyi da dama. An yi mata daurin talala a gida ba a kuma yanke mata wani hukunci ba, ganin halin da ta fada.
Inda aka samo: http://hausa.leadership.ng/2017/09/11/ganinku-ba-alheri-ba-shaidanun-mata-10-duniya/

Comments

Popular posts from this blog

'Women Tax Free' - The shop where men pay 7% more

Body Language :: Hand to face gestures

ABU/SBRS 2017-2018 SESSION REGISTRATION PROCEDURE