Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban EFCC Ibrahim Magu

Yan bindiga sun  kai hari gidan shugaban EFCC Ibrahim Magu
Ibrahim Magu
Wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan gonar shugaban hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati.
Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne ranar Talata da misalin karfe goma na dare.
Gidan gonar yana yankin karamar hukumar Karshi ne da ke wajen babban birnin tarayya.
Kakikin hukumar EFCC, Wilson Uwajuren da takwaransa na rundunar 'yan sandan Abuja, Anjuguri Jesse Manza sun ki tabbatar ko musanta aukuwar lamarin, a lokacin da BBC ta tuntube su.
Majoyoyinmu sun shaida mana cewa 'yan bindigar sun sace shanu da tumaki.
Sun kara da cewa shugaban na EFCC ya gina gidan da zai zauna a harabar gidan gonar, ko da yake bai kai ga tarewa a cikinsa ba har lokacin da aka ba shi shugabancin EFCC.
Wannan lamarin ya faru ne watanni da dama bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari a ofishin EFCC da ke unguwar Wuse Zone 7 da ke birnin na Abuja.
A wancan harin da aka kai a watan Agusta, 'yan bindigar sun yi ta harbe-harbe a cikin ofishin kafin su ajiye wata wasika da ke yin gargadin kashe wani babban jami'in bincike na EFCC, Ishaku Sharu.
Ibrahim Magu dai ya sha fama da mutanen da ake zargi da wawure kudaden Najeriya, a yunkurin da yake yi na ganin sun fuskanci hukunci.
Ya taba yin kira da a kafa kurkuku a dajin Sambisa domin a rika tsare wadanda suka aikata laifin cin hanci da rashawa a kasar
indana samu labarin;http://www.bbc.com/hausa/labarai-42323353

Comments

Popular posts from this blog

'Women Tax Free' - The shop where men pay 7% more

Body Language :: Hand to face gestures