An Tsare Jami'an Tsaro akan zargin Fyaɗe
Daga Munkaila T. Abdullah, Dutse Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Jigawa ta bada tabbacin tsare wani Jami’insu tareda wani jami’in hukumar tsaro na farin kaya (NSCDC) bisa zargin yiwa wata mata fyaɗe akan iyakar Nijeriya da Nijar dake ƙaramar hukumar Maigatarin jihar Jigawa. Kakakin rundunar ta ‘Yan sanda reshen jihar ta Jigawa, SP Abdul Jinjiri ya tabbatar da tsare waɗannan jami’an tsaro su biyu a ya yin zantawarsa da manema labarai a birnin Dutse.. Ya ce “Ya ce, babu ko shakka mun sami rahoton wannan badaƙala kuma tuni waɗanda ake zargi suna ɓangaren gudanarda bincike na wannan runduna tamu domin bibiya don binciko gaskiyar al’amari”. Haka kuma ya ƙara da cewa, wannan baiwar Allah ta gabatar da ƙorafinta ga cibiyar jami’anmu dake garin Maigatari wadda a yanzu haka an tsare waɗanda ake zargi domin gudanarda bincike. Sannan ya ce, tunidai rundunar ta tura jami’anta har wannan waje domin cigaba da bincike kuma matuƙar aka tabbatar da faruwar wannan al’amari to ...